TOP 10 SECRET CODING TIPS TO MAKE YOUR PROGRAMMING JOURNEY EASIER

yan'uwa albishirinku ga wasu sirruka manya guda goma da zaka bi domin ka samu saukin fahimtan programming language da kake koya, ga sunan kaman haka;

Na farko: Clear basics
wato abinda wannan yake nufi mutum bazai taba zama programmer bah face sai ya fahimci ginshin wannan yaren programming da yake koya. idan mutum ya koyi mafarin yaren programming irinsu data structures, variables, control structures etc to mutum zai samu saukin koyan programming.

Na biyu: Practice, not read
idan mutum yana koyan programming yana da kyau ya ringa yin karatu amma kada karatunsa yafi gwajinsa yawa, ya fifita yawan gwaji akan karatu domin da yawan gwaji neh ake zama kwararre harma ana cewa practice make perfect wato gwaji yana sa mutum ya zama kwararre.

Na Uku: Code by hand
idan mutum yana so ya zama kwararre a programming yana da kyau ya rubuta code din akan paper kafin ya rubuta shi akan na'urarsa domin duk abinda aka rubutashi a hannu kuma aka sake yin gwajinsa a na'ura zayi wahala mutum ya mantashi.

Na Hudu: Sharing knowledge
hanya mafi dacewa na koyan programming shine sanarda wasu akan abinda ka koya. domin idan kan koyarda waninka tamkar kana koyarda kanka neh.

Na Biyar: Taking breaks
yana da kyau ka huta idan ka gaji, ba'a so kata kurawa kanka domin zama agaban computer awa da awanni ba tareda hutawa yana janyo matsalar rashin fahimta, idan kaji barci ka kwanta kayi barci domin ka samu kwakwalwarka ta zama fresh.

Comments

Popular posts from this blog

Gabatarwa Akan YerwaTech

BAYANI AKAN WEBCODE DA KUMA YADDA AKE SAUKE SHI

TOP 5 PROGRAMMING LANGUAGES SET TO RULE THE MARKET BY 2030 ARE FUTURE OF TECHNOLOGY